2020-02-02 16:30:12 cri |
Yanzu kamfanonin kasar Sin masu samar da abin rufe baki, da rigar kariya daga kwayoyin cuta, da ruwan kashe kwayoyin cuta, suna kokarin inganta ayyukansu na samar da kayayyakin, don samar da isassun kayayyakin da ake bukata ga wurare masu fama da annobar, kamar yadda wasu hukumomin kasar ke kayyadewa.
A nata bangare, ma'aikatar zirga-zirga da sufuri ta kasar Sin ta sanar a jiya Asabar cewa, ya kamata a yi kokarin tabbatar da saukin jigilar wasu muhimman kayayyakin da ake bukata ba tare da wata matsala ba, inda ba za a dakatar da motoci masu dauke da kayayyki don gudanar da bincike a kansu ba, kuma ba za a karbi kudi kan yadda motocin suke amfani da hanyoyi ba. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China