Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan kasar Sin ya kira taron shugabanni masu kula da aikin tinkarar cutar numfashi
2020-02-02 21:38:03        cri
A yau Lahadi, firaministan kasar Sin, kana shugaban tawagar dake jagorantar aikin dakile cutar numfashi mai yaduwa, Li Keqiang, ya kira taron tawagar, domin tattauna karin matakan da za a dauka a kokarin dakile cutar, inda aka bukaci wasu lardunan kasar, da su tabbatar da aikin hana yaduwar annobar, gami da samar da isassun kayayyakin da ake bukata, musamman ma a fannin samar da kayayyakin aikin jinya, da sauran kayayyakin kariya ga birnin Wuhan, da sauran wuraren dake makwabtaka da shi, inda aka fi fama da cutar numfashin mai yaduwa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China