2020-02-02 16:32:53 cri |
Jami'in ya gayawa manema labaru cewa, yanayin kasuwar hada-hadar kudi tana samun sauye-sauye, yayin da ake fuskantar wani yanayi mai hadari, wannan ya dace da tsare-tsaren ayyukan kudi. Saboda haka, ba za a yi mamaki ba ganin yadda annobar "Novel Coronavirus Infection" ta yi tasiri kan yanayin kasuwar hada-hadar kudi ta kasar Sin. Sai dai hakan, a cewar jami'in, ba zai dade ba, domin ainihin abun da ya tabbatar da yanayin kasuwar shi ne ingancin tattalin arziki da harkokin hada-hadar kudi na wata kasa. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China