Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Sabbin wadanda suka kamu da cutar numfashi ta coronavirus sun kai 2,829
2020-02-03 10:36:46        cri
Hukumomin lafiya na kasar Sin sun ba da rahoton kamuwar karin mutane 2,829 da cutar numfashi ta coronavirus, sun kuma ce cutar ta hallaka karin mutane 57 a ranar Lahadi. Wannan adadi dai ya shafi karin wadanda suka harbu da cutar daga yankunan lardunan kasar 31 da kuma rukunin ma'aikata sojoji masu ba da taimako a jihar Xinjiang.

Cikin jimillar mamatan hadda mutum 56 daga lardin Hubei inda cutar ta fara bayyana, da mutum guda daga lardin Chongqing na kudu masu yammacin kasar. Kaza lika akwai sabbin wadanda ake shakkarsu da kamu da cutar da yawan su ya kai 5,173.

A daya hannun kuma, hukumar lafiyar kasar ta ce ya zuwa jiya Lahadi, yawan wadanda suka kamu da cutar, suke kuma cikin matsanancin hali ya kai mutum 186, yayin da mutane 147 suka warke, aka kuma sallame su daga asibiti.

Hukumar ta tabbatar da cewa, tun bullar cutar zuwa ranar Lahadi, adadin wadanda suka harbu da ita sun kai mutum ya kai 17,205, ta kuma hallaka jimillar mutum 361. Har ila yau, jimillar wadanda ke cikin halin mutu-kokwai-rai kokwai sun kai 2,296, yayin da ake tantance mutum 21,558 don tabbatar da ko sun kamu da cutar ko a'a. Har ila yau adadin jimillar wadanda aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar sun kai mutum 475. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China