2020-02-02 20:14:42 cri |
A cewar Madam Margaret Chan, bayan barkewar cutar numfashin, gwamnatin kasar Sin ta dauki kwararan matakai ba tare da wani jinkiri ba, haka kuma tana bayyana dukkan bayanan da ta samu a fili. Yanzu dukkan jama'ar kasar Sin na kokarin taimakawa aikin dakile cutar numfashin, karkashin jagorancin gwamnatin kasar, wannan a cewar Madam Chan ba wani abu da aka saba gani a sauran kasashen duniya ba ne.
Ban da haka Madam Chan ta jinjinawa masu nazarin kimiyya da fasaha na kasar Sin, inda ta ce masanan kasar Sin sun yi nazari kan kwayoyin cutar "Novel Coronavirus", gami da samun cikakkun bayanansu cikin sauri. Sa'an nan sun raba sakamakon nazarin ga hukumar WHO gami da takwarorinsu na kasashe daban daban. Ta haka sun taimakawa masanan kasashe daban daban fahimtar halayyar musamman ta kwayoyin cutar da suka haddasa annoba a wannan karo. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China