Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban majalisar mulkin Sudan ya samu gayyatar gwamnatin Amurka
2020-02-03 10:00:35        cri

A jiya Lahadi shugaban majalisar mulkin kasar Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya karbi goron gayyatar ziyarta a kasar Amurka. Sanarwar da majalisar mulkin kasar ta fitar ta ce, sakataren harkokin wajen Amurkar Mike Pompeo shi ne ya gayyaci shugaban gwamnatin na Sudan a yayin tattaunawarsu ta wayar tarho inda ya nemi ya je Amurkar domin sake nazarin huldar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da nufin kyautata alakar dake tsakanin sassan biyu.

Sanarwar ta ce, shugaban majalisar mulkin Sudan ya yi maraba da goron gayyatar, kuma ya yi alkawarin amsa gayyatar nan ba da jimawa ba.

Kasar Sudan ta jima tana menan Amurka ta tsame ta daga cikin jerin kasashen da Amurkar ta bayyana a matsayin kasashen dake daukar nauyin ayyukan ta'addanci.

Amurka ta fara sanyawa Sudan takunkumin tattalin arziki a shekarar 1997 kana ta ayyana kasar cikin jerin kasashen duniya dake tallafawa ayyukan ta'addanci tun daga shekarar 1993.

Sai dai kuma, a shekarar 2017, Amurka ta yanke shawarar janyewa kasar Sudan takunkumin tattalin arziki, amma ba ta tsame kasar daga cikin masu taimakawa ta'addanci ba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China