Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sudan ya sha alwashin hukunta wadanda suka hallaka alumma
2019-12-26 11:19:40        cri

Firaministan kasar Sudan Abdalla Hamdok, ya sha alwashin gurfanar da wadanda suka aikata kisan kai, da kisan kiyashi, yakin zanga-zangar da ta kai ga hambarar da tsohuwar gwamnatin kasar gaban kuliya.

Abdalla Hamdok ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, yayin da yake jawabi ga dandazon taron cika shekara guda da aukuwar zanga-zangar kasar ta watan Disambar bara, yana mai cewa ko shakka babu shari'a za ta yi halin ta.

Firaministan ya kara da cewa, gwamnatin kasar mai ci, za ta yi aiki tukuru, wajen tabbatar da cewa an hukunta dukkanin wadanda suka aikata muggan laifuka, tare da dawo da kimar iyalan wadanda hakan ya shafa.

A daya hannun kuma, Mr. Hamdok ya nanata muhimmancin cimma nasarar wanzar da zaman lafiya a Sudan, yana mai cewa idan babu adalci da zaman lafiya mai dorewa, manufar zanga-zangar da ta gabata ba za ta cika ba.

A ranar 19 ga watan Disambar nan ne dai al'ummar Sudan, ke murnar cika shekara guda da barkewar zanga-zangar da ta haifar da juyin juya halin kasar na ran 19 ga watan Disambar shekarar 2018. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China