Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadarin jirgin sama a yammacin Darfur na Sudan ya halaka mutane 18
2020-01-03 09:08:59        cri
Rahotanni daga Sudan na cewa, wani jirgin saman soja ya yi hadari jiya Alhamis jim kadan bayan tashinsa daga filin jiragen sama na El Geneina dake yammacin jihar Darfur na kasar Sudan, inda ya halaka mutane 18.

Wata sanarwar da rundunar sojojin kasar ta fitar ta bayyana cewa, hadarin ya rustsa da ma'aikatan jirgin 7, da alkalai 3, da wasu fararen hula 8 ciki har da kananan yara 4. Yanzu haka an fara gudanar da bincike don gano musabbabin hadarin.

Da farko dai jirgin ya kaiwa kungiyar Red Crescent ta Sudan dake El Geneina,babban birnin jihar yammacin Darfur kayayyakin kiwon lafiya ne. A 'yan kwanakin da suka gabata dai, birnin El Geniena ya sha fama da fadan kabilancin da ya yi sanadiyar mutuwa ko jikkatar mutane da dama.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China