Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar gudanarwa mulkin Sudan ta nada sabon jami'in hukumar leken asirin kasar
2020-01-17 10:20:40        cri
Shugaban majalisar gudanar da mulkin kasar Sudan Abdel Fattah al-Burhan a jiya Alhamis ya sanar da nada Jamal Abdul-Majeed a matsayin sabon shugaban hukumar leken asirin kasar (GIS), majalisar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta ce majalisar ta amince ta takardar yin murabus din da laftanal janar Abu-Bakr Dambalab ya gabatar don sauka daga mukamin babban daraktan hukumar ta GIS inda aka nada janar Jamal Abdul-Majeed a matsayin wanda zai gaje shi.

Matakin ya zo ne kwanaki biyu bayan boren da wasu daga cikin dakarun hukumar ta GIS suka yi.

A ranar Talata ne, helkwatar hukumar ta GIS ta fuskanci mummunar musayar wuta, wanda ya jefa al'ummar kasar cikin fargaba musamman mazauna shiyyar tsakiyar birnin Khartoum.

Gwamnatin Sudan ta bayyana lamarin a matsayin yunkurin juyin juya hali da dakarun tsaron suka yi.

A watan Augasta tsohuwar majalisar sojoji mai mulkin kasar ta rusa hukumar gudanarwar GIS. Inda aka yi kiyasin sallamar tsoffin ma'aikata 13,000 wadanda aka ba su zabi ko dai su shiga cikin aikin soji ko kuma su shiga cikin masu tallafawa dakarun tsaron kasar, ko kuma a sallame su daga aiki kana a biya su hakkokinsu na ritaya daga aiki.

Mafi yawa daga cikinsu sun amince da bukatar, yayin da wasu daga cikinsu suka ki amincewa su mika makamansu har sai an biya su hakkokin nasu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China