Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wata kotu a Sudan ta yankewa jami'an tsaron kasar 27 hukuncin kisa saboda kashe masu bore
2019-12-31 10:00:55        cri
A jiya ne wata kotu a kasar Sudan ta yankewa dakarun tsaron kasar su 27 hukuncin kisa, bisa zarginsu da kashe wani mai zanga-zangar da aka tsare a watan Fabrairu. Haka kuma, alkalin kotun ya yankewa wasu da ake tuhuma su uku hukucin daurin shekaru uku a gidan yari, yayin da aka sallami wasu guda bakwai.

A ranar 2 ga watan Fabrairu ne, rundunar 'yan sandan kasar ta Sudan, ta sanar da mutuwar Ahmed Al-Khair Ahmed, wani malamin makaranta da aka tsare a garin Khashm el-Girba a jihar Kassala dake gabashin kasar, bayan boren, wanda daga bisani ya gamu da ajalinsa bayan ya ci wani abinci mai guba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China