Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana da imani da karfin yakar cutar numfashin da ta bulla a kasar
2020-01-31 15:50:21        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana cewa, kasarta tana da imani da ma karfin yakar cutar numfashin da ta bulla a kasar.

Hua ta bayyana haka ne, yayin taron manema labarai da ya gudana a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, bayan da hukumar lafiya ta duniya(WHO) ta ayyana cutar da kwayar Coronavirus ke haddasawa a matsayin barazana ga harkokin kiwon lafiyar kasa da kasa.

Ta ce, tun lokacin da cutar ta barke, gwamnatin kasar Sin ta dauki managartan matakan kandagarki da hana yaduwar cutar, kuma da dama daga cikin wadannan matakai sun cika ka'idojojin lafiya na duniya. A don haka, kasar Sin da daukacin Sinawa na da imani da karfin ganin bayan wannan cuta baki daya. Haka kuma bangaren kasar Sin ya sanar da dukkan bangarorin da abin da ya shafa, yana kuma musayar bayanai game da kwayar cutar ba tare da wata rufa-rufa ba.

Ta ce, WHO da sauran kasashe da dama, sun yaba da matakan da kasar Sin ta ke dauka kan yaki da wannan annoba. Kuma kasar Sin tana tuntuba da ma yin hadin gwiwa da WHO.

A kwanakin baya ne kwararru daga WHO suka ziyarci birnin Wuhan, bayan da shi ma babban darektan hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ziyarci kasar ta Sin, inda ya tattauna da shugabannin kasar game da matakan yaki da cutar.

Madam Hua ta ce, Tedros ya yaba da matakan da kasar Sin ta ke dauka da ma irin gudummawar da ta ke baiwa duniya a yakin da ake yi da cutar Coronavirus. Tana mai cewa, kasarta za ta ci gaba da yin aiki da WHO da sauran kasashe, don ganin an kare lafiyar al'umma a matakin shiyya da ma duniya baki daya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China