Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sarauniyar Ingila ta amince da bukatar dakatar da aikin majalisar dokokin kasar da firaminita Boris Johnson ya gabatar
2019-08-29 11:38:23        cri

A gabannin ranar 31 ga watan Oktoba, ranar cika wa'adin janye jiki daga kungiyar Turai da Birtaniya ke kokarin cika, Sauraniyar Ingila Elizabeth II ta amince da bukatar da firaminista Boris Johnson ya gabatar kan dakatar da aikin majalisar dokokin kasar a yayin taron hukumar koli ta bada shawara ga sarauniyar da aka yi a ranar 28 ga wata.

Bisa shirin da aka tsara, majalisar dokokin kasar Birtaniya wadda ke cikin lokacin hutunta na zafi za ta kaddamar da aiki a ranar 3 ga wata mai zuwa. Bisa rokon da Johnson ya gabatar, Sarauniya Elizabeth II ta zartas da sake dakatar da aikin majalisar daga ranar 9 zuwa 12 ga watan Satumba, har zuwa ranar 14 ga watan Oktoba.

Wannan sabon shirin da Johnson ya tsara ya haddasa cece-kuce. Masu adawa na ganin cewa, an yi hakan ne domin hana ' yan majalisar su nuna rashin yarda da kudurin janye jiki daga EU ba tare da daddale kowace yarjejeniya ba. Mataimakin shugaban jam'iyyar hamayya ta Labor Tom Watson ya ce, lamarin mai matukar kaduwa ya keta tsarin demokuradiyya kiri da muzu.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China