Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Boris Johnson ya zama firaministan Birtaniya
2019-07-25 10:19:36        cri

An zabi sabon shugaban jamiyyar Conservative, Boris Johnson, kuma ya zama firaministan kasar Birtaniya tun daga ranar Laraba, a daidai lokacin da kasar ke cikin halin rashin tabbas game da batun ficewarta daga kungiyar tarayyar turai.

Hakan ya biyo bayan murabus din da Theresa May ta yi ne daga shugabancin kasar, kana sarauniyar Ingila ta gayyaci mista Johnson domin ya shugabanci gwamnatin Birtaniyar.

Johnson, tsohon sakataren harkokin wajen Birtaniya ne, kuma tsohon magajin garin birnin Landan, ya zama firaministan Birtaniya yayin cikar wa'adin ficewar kasar daga kungiyar tarayyar turai, kana a daidai lokacin da kasar ke fama da yanayin rashin tabbas.

Wasu masu zanga-zanga sun toshe hanya inda suka dakatar da motar da mista Johnson ke ciki a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa fadar Buckingham.

Shugaban jamiyyar adawa ta Labor, Jeremy Corbyn, ya bukaci a gudanar da babban zabe a kasar, yana mai cewa, sabon firaministan bai cancanci ya jagoranci al'ummar kasar Birtaniya ba.

Gabanin Johnson ya zama firaministan kasar, Philip Hammond, ya aje mukaminsa na shugaban hukumar tattara kudaden harajin kasar, kuma wannan shi ne ajiye aikin wani babban jami'in kasar mafi girma.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China