Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mahukuntan kasar Sin sun jaddada bukatar samar da kulawa ga wadanda suka kamu da cutar numfashi da ta bulla a kasar
2020-01-30 16:14:45        cri
Mahukuntan kasar Sin sun jadadda bukatar kula da wadanda suka kamu da cutar numfashi da ta bulla a kasar da ma samar da muhimman kayayyakin lafiya da ake bukata.

An dauki wannan mataki ne yayin taron da firaministan kasar Li Keqiang ya jagoranta jiya Laraba, kan yadda za a dauki matakan kandagarki da ma hana yaduwar cutar.

Taron ya bayyana cewa, tuni matakan sun fara aiki, duk da cewa an karfafa su, amma kuma cutar tana ci gaba da yaduwa, inda ta yi kamari a wasu yankunan kasar.

A cewar taron babban kwamitin tsakiya na JKS game da kandagarki da hana yaduwar cutar, yanayin yana da sarkakiya. A don haka, taron ya bukaci a kawar da kananan asibitoci, a samar da tsarin kula da marasa lafiya na bai daya, sannan a tura marasa lafiya dake cikin yanayi mai tsanani zuwa asibitoci masu inganci ko kuma kwararru dake sassan kulawar gaggawa su rika kula da su.

Bugu da kari, taron ya lura da cewa, ya kamata a hanzarta samar da maganin cutar, a kuma amince da magunguna da tun farko suka yi tasiri yayin da aka gwada su, don fara amfani da su ba tare da bata lokaci ba.

Haka kuma taron, ya bukaci gwamnatocin kananan hukumomi, da su tara kamfannoni, don dawo da aikin samar da muhimman kayayyaki kamar rigunan kariya da ma'aikatan lafiya ke bukata, da abubuwan rufe baki da hanci da magunguna.

Sauran sun hada da daukar matakan kandagarki da hana yaduwar cutar, yayin da jama'a ke dawowa wuraren ayyukansu, bayan bikin bazara. Daga karshe, taron ya ce ya kamata a jinkirta lokacin dawowa bakin aiki idan akwai bukatar haka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China