Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane miliyan 30 sun kalli yadda ake gina asibitoci a birnin Wuhan kai tsaye
2020-01-29 16:48:51        cri

A yau Laraba da karfe 3 a safe agogon wurin, mutane sama da miliyan 30 sun kalli yadda ake gina asibitocin Huoshenshan da na Leisheshan a birnin Wuhan kai tsaye ta manhajan hoton bidiyo na Yangshipin na babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice.

 

 

An soma gina asibitocin biyu ne a ranar 23 da 25 ga wata daya bayan daya, da nufin dakile yaduwar cutar numfashin da kwayar cutar coronavirus ke haddasawa, inda za a kwantar da wadanda suka kamu da cutar.

Ba kamar shirye-shiryen nishadi da labaru da ake saba gabatarwa ba, a wannan karo ba a yi bayani ko sanya kide-kide a yayin da ake watsa shirin ba, amma duk da haka, ya jawo hankalin'yan kasar da dama masu bibiyar yanar gizo, har ma sun yi ta yi musayar ra'ayoyi game da haka.

 

 

Masana suna ganin cewa, watsa yadda ake gina asibitocin kai tsaye ya samar da wani dandamali ga masu kallon yanar gizo wajen saukaka zaman zullumi da ma damuwa tsakanin jama'a. sakamakon tsayawa a cikin gida a wannan lokacin hutun na musamman, a sa'i daya kuma, ya bayyana fatan Sinawa na kawo karshen annobar cutar cikin sauri, da kara warkar da wadanda suka kamu da cutar, Don haka, yake jawo masu kallo fiye da miliyan 30. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China