Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta dauki jerin matakan yin rigakafi da shawo kan cutar numfashi
2020-01-27 17:12:47        cri

Domin karfafa ayyukan kandagarki, da shawo kan cutar numfashi da kwayoyin cutar coronavirus ke haifarwa, ofishin majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da sanarwa a yau Litinin, mai kunshe da tsawaita lokacin hutu na bikin bazara na bana, zuwa ranar 2 ga wata mai zuwa, wato za a koma bakin aiki a ranar 3 ga watan Fabrairu.

Kwalejoji da jami'o'i, da makarantun firamare, da na sakandare, da gidajen renon yara na wurare daban daban na kasar Sin kuwa, za su jinkirta lokacin fara zangon karatu. Hukumar ba da ilmi za ta a sanar da hakikanin lokacin fara karatu a nan gaba.

A yayin taron watsa labarai, wanda hukumar lafiyar kasar ta Sin ta shirya a yau, manazarcin cibiyar ayyukan kandagarki, da shawo kan cututtuka ta kasar Sin Feng Luzhao ya ce, cutar numfashin ta coronavirus, cuta ce da ke shafar sassan jiki masu taimakawa numfashi, kuma taba ruwan da ya fito daga baki da hanci mai dauke da cutar ne kadai babbar hanya ta yaduwarta tsakanin al'umma. Don haka, hana fita waje, da taruwar jama'a, muhimmin mataki ne na hana yaduwar cutar.

An tsaida kudurin tsaiwaita lokacin hutu ne domin karfafawa jama'a gwiwar zama a gida, da dakile shiga yankunan da aka fi samun yaduwar cutar, da wuraren taruwar jama'a, duka dai da nufin rage hadarin kamuwa da cutar. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China