Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta kakkaba sabbin takunkumai kan Iran duk da kiraye-kirayen da kasashen duniya ke yi na a kai zuciya nesa
2020-01-11 16:11:37        cri
Duk da kiraye-kirayen kasashen duniya na a kai zuciya nesa, gwamnatin Amurka ta sanar da kakkaba sabbin takunkumai kan Iran a jiya Juma'a.

Sakataren kudin Amurka Steven Mnuchin, ya shaidawa manema labarai jiya a Fadar White House cewa, takunkuman sun shafi bangaren sarrafa karafa da sauran bangarorin tattalin arzikin Iran.

Steven Mnuchin, ya kara da cewa, ma'aikatarsa ta kuma ware wasu manyan jami'an Iran 8 da aka kakkabawa takunkumi, ciki har da Ali Shamkhani, sakataren majalisar kolin kasar mai kula da harkokin tsaro da kuma Mohammad Reza Ashtiani, mataimakin babban hafsan sojin kasar.

Cikin wata sanarwar da ma'aikatar kudin Amurka ta fitar, ta ruwaito Steven Mnuchin na ikirarin Amurka ta kakkabawa jami'an 8 takunkumi ne, saboda da hannu da suke da shi a hare-haren makamai masu linzami da aka harba kan sansanonin Amurka a ranar Talata.

Har ila yau, cikin sanarwar da fadar White House ta fitar jiya Juma'a, Shugaban kasar, Donald Trump, ya ce manufar takunkuman ita ce, hana Iran samun kudin shigar da za ta yi amfani da su wajen samar da kudi ga shirinta na nukiliya da sarrafa makamai masu linzami da daukar nauyin ayyukan ta'addanci da tasirinta a yankin.

Duk da yanayin da ake ciki, kasashen duniya na kira ga dukkan bangarori da su kai zuciya nesa tare da cimma maslaha. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China