Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 17 sun mutu 14 sun samu raunuka a hadarin mota a arewa masu yammacin Najeriya
2020-01-21 09:54:50        cri
Baki daya mutane 17 ne suka mutu kana wasu mutanen 14 suka samu raunuka a sakamakon hadarin mota a ranar Litinin a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, hukumar 'yan sandan kasar ta sanar da faruwar lamarin.

Hadarin ya faru ne a kauyen Yardudu dake karamar hukumar Mashi na jihar Katsina dake arewa maso gabashin Najeriya.

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah, ya ce suna cigaba da gudanar da binciken musabbabin hadarin.

Jami'in 'yan sandan yac e sakamakon farko na binciken ya nuna cewa, direban babbar motar daukar kaya dake kan hanyarsa ta zuwa Legas ne ya gaza sarrafa motar a babbar hanyar motar. Motar dai ta yi lodin shanu ne da kuma wasu fasinjoji.

Ya ce kan babbar motar ya balle daga jikin bodin motar, inda ya fada karkashin wata gada, lamarin da ya haifar da mummunar hasara. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China