Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An hallaka mayakan Boko Haram masu yawa a arewa maso gabashin Najeriya
2020-01-05 15:36:37        cri
Kakakin rundunar sojojin saman Najeriya ya ce an hallaka mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram a wasu hare-hare ta jiragen sama da sojojin suka kaddamar a dajin Sambisa dake jahar Borno, a shiryyar arewa maso gabashin kasar.

An kaddamar da hare-haren a ranar Laraba a lokacin da jirgin saman yaki mallakin hukumar sojojin saman Najeriyar (NAF) ya yi lugudan wuta kan sansanin mayakan na Boko Haram a cikin dajin, kakakin hukumar ta NAF Ibikunle Daramola ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Ya ce dajin ya kasance wata maboya ga 'yan ta'addan inda suke shirya kai hare-hare a sansanin sojojin dake kusa da dajin, kana an ga wasu daga cikin 'yan ta'addan suna kokarin tura wasu motoci zuwa yankin.

Jiragen saman yakin na NAF masu yawa sun sha kaddamar da hare-hare a maboyar mayakan, inda suka hallaka mayakan na Boko Haram masu yawa da kuma lalata wuraren zamansu, in ji shi, sai dai ba su bayyana takamman adadin mayakan da suka hallaka ba

Daramola ya ce, dakarun sojojin saman za su ci gaba da kai hare-hare kan 'yan ta'addan a shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China