Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana fuskantar da yaduwar annobar cutar huhu, in ji jami'in kiwon lafiyar Sin
2020-01-23 13:49:54        cri

Ya zuwa karfe 24 na ranar 22 ga wata, kwamitin kiwon lafiya na kasar Sin ya samu rahoton gano mutane 571, wadanda aka tabbatar sun kamu da sabuwar annobar cutar huhu a larduna guda 25 na cikin kasar Sin, kuma mutane 17 sun rasu sakamakon cutar, dukkaninsu a lardin Hubei.

Ya zuwa yanzu, ana sa ido kan mutanen da suke da nasaba da wadanda suka kamu da cutar su dubu daya da dari hudu a asibitoci. Kuma ana fuskantar kalubalen ci gaba da yaduwar sabuwar annobar cutar huhun.  

Yayin taron manema labaran da aka ji a jiya Laraba, mataimakin shugaban kwamitin kiwon lafiya na kasar Sin Li Bin ya bayyana cewa, an gano karuwar masu dauke da cutar cikin sauri a baya bayan nan, sakamakon ingantattun dabarun gano ta, da sanadaran tabbatar da kamuwa da ita da ake da su. Ya ce, "A baya bayan nan, adadin masu dauke da cutar na karuwar cikin sauri, sakamakon ingantattun dabarun gano cutar, da sanadaran tabbatar da kamuwa da ita da ake da su. Kwararru suna ganin cewa, dukkanin masu dauke da cutar suna da nasaba da birnin Wuhan, kuma yanzu, cutar tana yaduwa tsakanin mutane, ciki hadda jami'an kiwon lafiya da suka kamu da cutar. Ana ganin cewa, cutar tana iya yaduwa a tsakanin al'ummomi mazauna unguwanni. Cutar tana kuma yaduwa ta hanyar numfashi, kuma akwai yiwuwar samun canjin samfurin halittar ta, wanda hakan ke haddasa kalubale na ci gaba da yaduwar ta. A halin yanzu, ana cikin wani musamman lokaci na zirga-zirgar fasinjoji kafin fara bikin bazara, lamarin da ya kara tsananta kalubalen yaduwar cutar, da kuma shiga cikin mawuyacin hali game da kandagarkin cutar, dole ne mu mai da hankali matuka kan wannan batu. "

Yanzu, an shiga lokaci mafi samun tafiye-tafiyen mutane tsakanin wurare daban daban a kasar Sin kafin bikin bazara. Li Bin ya ce, harkar ta kawo matsaloli wajen aiwatar da matakan dakile yaduwar cutar. Shi ya sa, kwamitin kiwon lafiyar kasar Sin, ya kafa tsarin yin hadin gwiwar hana yaduwar cutar, domin daukar matakai na daban a wurare na daban. Yana mai cewa, "A wuraren da suka riga suka samu yaduwar cutar, za a karfafa aikin sa ido, domin gano masu dauke da ita cikin sauri, za a shigar da su asibiti cikin gaggawa, a kuma samar musu jinya cikin sauri, a nan kalmar "sauri" tana da muhimmanci kwarai da gaske. Sa'an nan kuma, ya kamata mu samar wa wuraren karin kayayyakin kula da lafiya, da karfafa aikin ba da jinya ga masu dauke da cutar, da kuma sa ido kan wadanda suke da nasaba da masu dauke da ita. A wuraren da ba a samu masu dauke da cutar ba kuma, ya kamata mu tsara aikin fuskantar yanayin gaggawa. Sa'an nan, a tanadi motoci masu daukar marasa lafiya, da kebe dakunan kwanciya, a nemi likitoci masu ba da jinya kan cutar, da magunguna da dai sauransu, domin fuskantar yaduwar cutar. A karshe, ya kamata mu fara ba da horo ga masu aikin likitanci, da masu aikin jinya, domin tabbatar da cewa, an aiwatar da matakai yadda ya kamata, a lokacin da aka gano wasu dake dauke da wannan cuta."

Kuma bisa labarin da kwamitin kiwon lafiyar birnin Wuhan ya fidda, an ce, yanzu, akwai masu aikin likitanci da suka kamu da wannan cuta, sakamakon kulawa da suka yi da masu dauke da ita. Dangane da wannan lamari, mataimakiyar shugaban hukumar harkokin likitanci na kwamitin kiwon lafiyar kasar Sin Jiao Yahui ta bayyana cewa, za a dauki karin matakan kandagarki, domin ba da jinya mai inganci ga masu dauke da cutar, da kuma kiyaye tsaron masu aikin likitanci.

Bayan barkewar cutar, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da labarai game da yaduwar sabuwar annobar cutar ta huhu ga kungiyar kiwon lafiyar kasa da kasa ta WHO, da kungiyoyin kasa da kasa da na shiyye-shiyya, da ma yankunan Hong Kong, da Macao da Taiwan na kasar Sin cikin sauri. Ta kuma fara yin mu'amala da hadin gwiwa da bangarorin da abun ya shafa, domin hana yaduwar cutar. Li Bin ya ce, "Muna mu'amala da kungiyar WHO, kan yanayin sabuwar annobar cutar huhun, da yadda ake gudanar da ayyukan hana yaduwar cutar ta a duk fadin kasar Sin, da kuma gabatar wa kungiyar tsarin kwayoyin cutar, har ma mun kafa tawagar musamman, domin karfafa musayar ra'ayoyi a tsakanin kwararrun Sin da na kungiyar WHO. Mun kuma yi hira da ofisoshin jakadanci, da hukumomin fasahohi na kasashen Thailand, da Japan, da Koriya ta Kudu da Amurka da dai sauransu, domin yin musaya kan yanayin yaduwar cutar, da kuma tabbatar da labarai game da masu dauke da ita. Ban da haka kuma, kwamitin kiwon lafiya ya riga ya gayyaci kwararrun kungiyar WHO, da na yankunan Hong Kong, da Macao da Taiwan na kasar Sin, su je birnin Wuhan, su yi mu'amala da likitocin birnin."

A nan gaba kuma, Li Bin ya ce, gwamnatoci da hukumomin kiwon lafiya na wurare daban daban, za su ci gaba da mai da hankali kan birnin Wuhan, da kuma karfafa ayyukan yin rigakafi. A sa'i daya kuma, za a ci gaba da karfafa matakan yin rigakafi, da sa ido a duk fadin kasar Sin, a lokacin zirga-zirgar fasinjoji na bikin bazara, da kuma gabatar da labarai game da cutar cikin lokaci, yayin da ake inganta aikin nazari da yin mu'amala da kwararrun kasa da kasa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China