Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kawarru: Sin na kan wata muhimmiyar gaba ta dakile yaduwar cutar numfashi da ta bulla
2020-01-22 11:40:24        cri
Kwararru a fannin kiwon lafiya na kasar Sin, sun ce kasar na kan wata muhimmiyar gaba ta dakile yaduwar cutar nan ta numfashi da ta bulla a wasu sassan kasar.

Cikin matakan da ake dauka yanzu haka, hadda na kandagarkin yaduwar cutar, inda tuni aka fidda bayanai game da yanayin kwayoyin halittar cutar, a wani mataki na tallafawa masu bincike, da hukumomin lafiya, ta yadda za su iya kaiwa ga samar da kayayyaki, da magunguna da ake bukata domin kawar da cutar.

A jiya Talata, hukumar lafiya ta kasar Sin ta bayyana cewa, ta kafa wani tsarin samar da kariya, da dakile yaduwar wannan cuta, inda sassan hukumomi 32 ke hadin gwiwar ganin an samar da maganinta, da dakile yaduwarta, da gudanar da binciken kimiyya a kanta da dai sauran su.

Har ila yau, an tsara yanayin fitar da bayanai na sabbin masu kamuwa da cutar numfashi ta "pneumonia". An kuma fara wallafa bayanai na rana rana, masu nasaba da wannan cuta a mataki na larduna, da yankunan kasar tun daga ranar Talata.

A daya hannun kuma, hukumar lafiyar ta ja kunnen dukkanin cibiyoyin kula da lafiya, da kada su ki karbar wadanda suka kamu da cutar "pneumonia", duba da cewa an tanaji isassun magunguna, da kayan bincike, da isassun kayan samar da kariya ga jami'ain lafiya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China