Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta daidaita shirin biyan kudaden jinya ga wadanda suka kamu da sabuwar annonbar cutar huhu
2020-01-22 11:44:10        cri
Gwamnatin Sin ta gabatar da wani shirin wucin gadi na biyan kudaden jinya ga mutanen da suka kamu da cutuka masu nasaba da sabuwar annobar cutar huhu da ta bulla don ba su kulawa a kan lokaci.

A cewar hukumar kula da lafiya ta kasa, dukkan kudaden magunguna da ayyukan jinya da aka kashe wajen magance cutar ta huhu, shirin inshorar lafiya ne zai dauki nauyin biyan dukkan kudaden.

Bangarorin shirin inshorar lafiyar za su biya kudaden maganin tun gabanin kammala jinyar da nufin magance matsalolin kudade ga asibitoci. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China