Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi sun kai mutum 440
2020-01-22 13:29:08        cri

Ya zuwa daren ranar Talata, an tabbatar da kamuwar mutane 440 da cutar numfashin nan, wadda kwayoyin cutar "novel coronavirus" ke haddasawa, a wasu yankuna 13 dake lardin Hubei na kasar Sin.

Tuni dai cutar ta hallaka mutane 9, dukkaninsu a lardin na Hubei, kamar dai yadda mataimakin daraktan hukumar lafiya ta kasar Sin Li Bin ya bayyana, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Larabar nan.

Ya ce bisa jimilla, a jiya Talata, an samu karuwar sabbin mutane 149 da suka harbu da wannan cuta. Kaza lika an tabbatar da kamuwar mutum guda a kasar Japan, da mutane 3 a Thailand, da kuma wani dan kasar Korea ta kudu daya.

Jami'in ya kara da cewa, an samu damar gano karuwar masu dauke da cutar ne a baya bayan nan, sakamakon ingantattun dabarun gano ta, da sanadaran tabbatar da kamuwa da ita da ake da su. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China