Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana fuskantar da yaduwar annobar cutar huhu, in ji jami'in kiwon lafiyar Sin
2020-01-23 13:06:43        cri
Ya zuwa karfe 24 na ranar 22 ga wata, kwamitin kiwon lafiya na kasar Sin ya samu rahoton gano mutane 571, wadanda aka tabbatar sun kamu da sabuwar annobar cutar huhu a larduna guda 25 na cikin kasar Sin, kuma mutane 17 sun rasu sakamakon cutar, dukkaninsu a lardin Hubei.

Ya zuwa yanzu, ana sa ido kan mutanen da suke da nasaba da wadanda suka kamu da cutar su dubu daya da dari hudu a asibitoci. Kuma ana fuskantar kalubalen ci gaba da yaduwar sabuwar annobar cutar huhun.(Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China