Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na da karfin zuciya kan hana yaduwar annobar cutar huhu
2020-01-21 15:16:59        cri

Kwanan baya, wata sabuwar kwayar cuta, dake cikin rukuni guda da annobar cutar huhu ta SARS da ta tafka barna shekaru 17 da suka wuce, ta yadu a wasu sassan birnin Wuhan na lardin Hubei na kasar Sin. Ya zuwa karfe 6 na yammacin ranar 20 ga wata, an kai rahoton gano mutane 224 da ake sa ran sun kamu da sabuwar annobar cutar huhu a kasar ta Sin, a ciki kuma an tabbatar da wasu 217 sun kamu da annobar. Kungiyar kwararru karkashin shugabancin kwamitin kiwon lafiyar kasar Sin sun bayyana a nan Beijing cewa, ana da karfin zuciya wajen hana yaduwar annobar. Matsalar da ta faru sakamakon yaduwar annobar cutar huhu ta SARS shekaru 17 da suka wuce ba za ta sake abkuwa ba.

A yammacin ranar 20 ga wata, kwararru karkashin shugabancin kwamitin kiwon lafiyar kasar Sin sun zanta da 'yan jaridu, inda daga fannin ilmin likitanci ne suka yi hasashe kan halin da ake ciki wajen yaki da wannan sabuwar annobar cutar huhu. Zhong Nanshan, shugaban kungiyar kwararrun, kana dan kwalejin ilmin injiniya na kasar Sin kuma darektan cibiyar nazarin cututtukan da suka shafi sassan jiki masu taimakawa numfashi ta kasar Sin ya bayyana ba tare da rufa-rufa ba cewa,"Wuraren da wadanda suka kamu da annobar suke ciki, suna da nasaba da kasuwar sayar da halittun teku ta Wuhan, inda aka samu barkewar annobar a wannan karo. Amma bayan rufe kasuwar, akwai karin mutanen da suka kamu da annobar. Yanzu an tabbatar da yaduwar annobar a tsakanin mutane. Sa'an nan kuma likitoci da nas 14 sun kamu da annobar sakamakon kulawa da masu dauke da annobar, lamarin da ya kasance a matsayin wata muhimmiyar alama. Annobar tana yaduwa tsakanin mutane."

Zeng Guang, mamban kungiyar kwararrun kuma babban mai ilmin kimiyya kan yaduwar cututtuka a cibiyar yin rigakafi da hana yaduwar cututtuka ta kasar Sin ya yi bayani da cewa, "Birnin Wuhan ya shiga matakin farko ne a fannin yaduwar wannan sabuwar annobar cutar hutu. Ya zuwa yanzu ba a gano matasa da kanana yara sun kamu da annobar ba tukuna. Yanzu yawancin masu fama da annobar, tsofaffi da kuma mutanen dake fama da cututtukan dake addabar mutum sannu a hankali ne. Ba a gano dimbin mutane sun kamu da annobar ba tukuna. Amma ya zama tilas mu yi taka tsan-tsan matuka. A ganina, muddin muka dauki matakai yanzu ba tare da bata lokaci ba, to za a iya hana bazuwar annobar, za a samu nasarar yaki da annobar."

Kwararrun sun jaddada cewa, dakatar da mutane masu zirga zirga daga birnin na Wuhan yana da muhimmanci sosai wajen hana yaduwar annobar. Haka kuma, muddin an yi zazzabi ko kuma yin tari da dai sauransu, sai a hanzarta ganin likita don samun magani, kana a kai masu fama da annobar wurin da aka kebe domin hana yaduwar annobar, ayi kokarin hana annobar yaduwa a tsakanin mutane. Zhong Nanshan ya ce, "Muna bada shawara cewa, kada a je Wuhan kuma kada a fito daga Wuhan, sai idan akwai wani muhimmin abu. Idan mun dauki matakai yadda ya kamata, to za a rage yiwuwar kasancewar mutanen da suka kamu da annobar."

Yanzu kwararrun suna gudanar da nazari kan annobar, yayin da ake bada magani ga masu fama da annobar. Kwararrun sun sake nanata cewa, kada a danne aikin yaki da annobar, sa'an nan kada a ji tsoro. Zhong Nanshan ya ce, "Ina da karfin zuciya sosai. Mummunan abin da ya faru sakamakon yaduwar annboar cutar huhu ta SARS a shekaru 17 da suka wuce ba zai sake abkuwa ba. Mun tabbatar da wannan sabuwar annobar cutar cikin makonni 2 kawai. Haka zalika muna aiwatar da manufar sa ido da kai masu fama da annobar wurin da aka kebe domin hana yaduwar annobar."

Kwararrun sun yi gargadi da cewa, dole ne a sha wanke hannu, a sanya abin rufe baki a wuraren da mutane suke taruwa. Kada a ci namun daji. A bar su zama a wuraren da suke zaune. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China