Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da shi ya karu da kashi 5.8% a shekarar 2019
2020-01-22 10:50:59        cri

Wani babban jami'in ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin, ya bayyana a wani taron manema labarai da ofishin watsa bayanai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira a jiya Talata cewa, a shekarar 2019, yanayin kasuwancin kasar Sin yana cikin daidaito, inda yawan kudin da suka shafi wannan bangare ya zama na farko a tsakanin kasashe masu tasowa, kuma na biyu tsakanin dukkan kasashen duniya.

Mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin Qian Keming ne ya bayyana haka a jiya Talata, inda ya kara da cewa, a shekarar 2019, kasar Sin ta samu damar yin amfani da jarin da wasu kamfanonin kasashen waje suka zuba mata, wanda yawansa ya kai Yuan biliyan 941.5 (kwatankwacin dalar Amurka biliyan 136.4), wanda ya karu da kashi 5.8% bisa na bara, kuma ya kai matsayin koli a tarihi.

Wannan adadi ya sa kasar Sin ta ci gaba da zama kasa mafi janyo jarin waje ta biyu a duniya. A cewar jami'in, ana ta kokarin inganta tsarin amfani da jarin waje a kasar Sin, yayin da wasu kasashen dake da tattalin arziki mai ci gaba, suke kokarin zuba karin kudade ga kasuwannin kasar. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China