Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNICEF ya yi kiyasin za a haifi jarirai dubu 26 a Najeriya a ranar sabuwar shekara
2020-01-02 10:45:06        cri
Asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF) ya yi kiyasin cewa, za a haifi jarirai 26,039 a Najeriya a farkon ranar sabuwar shekarar ta 2020.

Wakilin asusun dake Najeriya Peter Hawkins ne ya bayyana hakan, cikin wata sanarwar da kamfanin dillancin labarai ya samu kwafenta a Lagos, yana mai cewa, adadin jariran kasar zai kai kusan kaso 7 cikin 100 na yawan jarirai 392,078 da asusun ya yi hasashen za a haifa a duniya a ranar sabuwar shekarar 2020.

Hawkins ya ce, wannan adadi, shi ne adadin jarirai mafi yawa da za a haifa wannan rana a duniya, bayan kasar Indiya da za a haifi jarirai 67,385, sai kasar Sin da za a haifi jarirai 46,299 a wannan rana. Ya ce, yayin da aka shiga sabuwar shekara, asusun na UNICEF yana yin tuni cewa, kowane jariri ko jaririya a kasar, za su fara taka rayuwarsu ce kawai, idan an ba su damar rayuwa da bunkasa.

Wakilin ya ce, ga miliyoyin sabbin jariran da aka haifa a sassan duniya kuwa, ciki har da Najeriya, ranar haihuwar tasu alamu ce ta nasara. A cewarsa, a shekarar 2018, akwai jarirai miliyan 2.5 da aka haifa a sassa daban-daban na duniya wadanda suka mutu bayan wata guda da haihuwarsu, kuma kusan kaso ukun wannan adadi, sun mutu a ranar da aka haife su. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China