Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban hafsan sojojin kasan Najeriya ya yaba kwazon dakarun na yaki da Boko Haram
2020-01-02 10:55:36        cri
Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Tukur Buratai, ya yaba kwazon sojojin dake yaki da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

Babban hafsan sojojin ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai lokacin da ya ziyarci kwalejin horas da 'yan sanda dake garin Gwoza na jihar Borno, yana mai cewa, rawar da sojojin suke takawa a kasa da baki daya, abin a yaba ne da karfa gwiwa.

Buratai ya ce, sojojin sun nuna kwarewa da jajircewa game da yanayin wurin, sun kuma ci gaba da kaiwa maboyar 'yan ta'adda hari. Ya ce, manufar kafa sansanin ta yi nasara, ta kuma taimakawa sojojin kara fahimtar halayen 'yan ta'addan da ma samun galaba a kansu.

kwalejin horas da 'yan sandan dai, yana daya daga cikin muhimman cibiyoyin tsaro da mayakan na Boko Haram suka kwace, yayin da suke tsaka da kai hare-hare a jihar Borno a shekarar 2014. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China