2020-01-09 19:56:32 cri |
Shugaban hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman kasar Iran Ali Abedzadeh, ya sanar da cewa, akwatin nadar bayanan jirgin ya lalace. Ya bayyana a jiya cewa, jirgin ya bace daga na'urar rada, bayan ya tashi da nisan kafa dubu 8, daga bisani ya fado kasa, kuma matukin bai aike da wani sakon wata matsala ba.
Wurin da jirgin ya fado, ya nuna cewa, bayan da matukin ya gamu da matsala, sai ya yi kokarin dawo wa filin saukar jiragen.
Abedzadahe ya ce, akwai mutane 176 a cikin jirgin, wadanda suke kunshe da fasinjoji 167 da kuma ma'aikatan jirgin guda 9. (Ibrahim Yaya)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China