Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Javad Zarif ya zargi Amurka da neman mayar da hannun agogo baya
2020-01-10 11:03:19        cri
Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif, ya shaidawa taron kwamitin tsaron MDD cewa, wata kasa rudaddiyar guda daya, na neman mayar da hannun agogo baya, yana mai nuna yatsa ga Amurka.

Zarif, wanda Amurka ta hana VISAr shiga kasar domin halartar taron muhawarar majalissar ministocin harkokin waje na kwamitin tsaron MDD da ya gudana jiya Alhamis, ya ce matakin Amurka na baya bayan nan, kari ne kan munanan akidunta, da suka hada da daukar matsaya ta kashin kai, da watsi da ka'idoji da dokokin kasa da kasa, inda a baya bayan nan ta hallaka jarumin soja, da ya zame wa manyan kungiyoyin 'yan ta'adda kamar ISIS kadangaren bakin tulu.

Mr Zarif dai bai samu zuwa kafa da kafa taron na kwamitin tsaron MDD ba, wanda aka yiwa take da "Wanzar da yanayin zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, hanyar daga martaba dokokin MDD".(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China