Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Harajin kayan da ake shigarwa Amurka daga Sin na ratayuwa ne a wuyan Amurkawa, in ji Asusun IMF
2019-05-24 19:23:22        cri
Wani binciken da asusun ba da lamuni na IMF ya gudanar, ya nuna cewa harajin kayan da ake shigarwa Amurka daga Sin, na ratayuwa ne a wuyan Amurkawa dake safarar hajojin.

Sakamakon binciken da aka fitar a jiya Alhamis, ya nuna cewa, a baya harajin da Amurka ta sanya kan hajojin Sin ya rage hada hadar cinikayya tsakanin kasashen biyu, amma gibin cinikayyar dake tsakanin sassan biyu bai sauya sosai ba.

Kaza lika binciken ya nuna cewa, wani bangare na irin wannan haraji yana komawa ne kan Amurkawa masu sayayya, yayin da wani bangaren yake komawa wuyan 'yan kasuwar dake shigar da hajojin kasar, ta hanyar rage ribar da suke samu daga kasuwa.

An kuma nuna cewa, duk da cewa saurin bunkasar tattalin arzikin duniya na matsakaicin matsayi a halin yanzu, mai yiwuwa ne takaddamar cinikayyar da ake fama da ita yanzu haka, ta illata hada hadar cinikayya da kasuwar hannayen jari. Kana hakan na iya dakatar da ci gaban hada hadar hajoji a mataki na kasa da kasa, da karya lagon farfadowar tattalin arziki duniya cikin wannan shekara ta 2019. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China