Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mafi yawan Sinawa na da sha'awar shiga aikin sa kai na kare muhalli
2019-08-19 10:57:36        cri

Wasu alkaluma na binciken jin ra'ayin al'umma sun shaida cewa, kusan kaso 62 bisa dari na Sinawa na da sha'awar shiga a dama da su a fannin ayyukan kare muhalli.

Binciken da jaridar "China Youth Daily" ta gabatar ya nuna cewa, kusan kaso 55 bisa dari na wadanda aka ji ra'ayin su, su 2,000 sun bayyana burin su na shiga ayyukan raya al'umma, kana kaso 44 bisa dari na fatan ba da gudummawar su a fannin raya ilimi.

Cikin wadanda aka ji ta bakin su, wani dalibin kwaleji mai suna Gu Hui, ya ce ta hanyar gudanar da ayyukan al'umma, ya samu damar sanin mutane, da kara gogewa wajen juriya da hakuri.

Gu ya ce daga abubuwa da ya koya na zahiri, ya gano cewa, akwai bukatar jami'o'i su karfafa gwiwar dalibai, wajen shiga ayyukan amfanar da al'umma, ta hanyar sada su da ra'ayoyin sauran wadanda ke shiga irin wadannan ayyuka.

An tattara alkaluman ne dai daga amsoshin wadanda aka tuntuba, mafi yawanci wadanda aka haifa tsakanin shekarun 1980 zuwa 1990. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China