Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin manyan kasashen duniya sun yi kira ga kasashen waje su daina tsoma baki cikin harkokin Libya
2020-01-20 09:50:52        cri
Shugabannin manyan kasashen duniya dake halartar taro kan Libya a birnin Berlin na Jamus, sun yi kira da a kawo karshen tsoma bakin cikin rikicin Libya da kasashen waje ke yi, suna masu alkawarin kafa kwamitin da zai bibiyi sakamakon taron.

Shugabannin manyan kasashe masu fada a ji da sauran kasashen da batun ya shafa, sun hadu ne jiya Lahadi a Berlin, domin lalubo hanyar warware rikicin Libya cikin ruwan sanyi. Wakilai daga MDD da Tarayyar Turai da Tarayyar Afrika da Kungiyar kawancen kasashen Larabawa, da shuagabannin bangarorin adawa da suka hada da Khalifa Haftar, shugaban rundunar sojin yankin gabashin kasar da Fayez al-Sarraj, shugaban gwamnatin Libya da MDD ke marawa baya, su ma sun halarci taron.

Sanarwar bayan taron da aka fitar, ta ruwaito shugabannin na cewa, suna jadadda kudurinsu, na martaba cikakken iko da 'yanci da yankuna da hadin kan kasar Libya. Inda suka ce tsarin siyasa irin na kasar Libya, karkashin jagorancin kasar ne kadai zai iya kawo karshen rikicin da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Shugabannin sun ce suna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, su kauracewa duk wani abu da ka iya ta'azzara rikicin ko kuma sabawa takunkumin kwamitin sulhu ko shirin tsagaita bude wuta, ciki har da samar da kudade ga ayyukan soji ko horar da sojojin haya.

A cewar sanarwar, mahalarta taron sun yi kira da daukar managartan matakai, ta hanyar farawa da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da dukkan bangarorin suka cimma wadda za ta kai ga kawo karshen dukkan wasu hare-hare, ciki har da wadanda ake kai wa ta saman yankunan kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China