Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojojin kasar Libya mai sansani a gabashin kasar ta kwace Sirte
2020-01-07 12:48:47        cri
Rundunar sojojin kasar Libya mai sansani a gabashin kasar ta kwace Sirte dake gabar teku daga hannun gwamnatin Libya mai samun goyon bayan MDD. A nata bangaren, gwamnatin kasar mai samun goyon bayan MDD ba ta mai da martani ba tukuna.

An ce, birnin Sirte ya dade yana hannun kungiyar IS, kafin sojojin gwamnatin Libya mai samun goyon bayan MDD ta karbe shi a watan Disambar shekarar 2016.

A watan Afrilu na shekarar 2019, rundunar sojojin kasar Libya mai sansani a gabashin kasar ta kai hari kan birnin Tripoli, ta kuma yi musanyar wuta da sojojin gwamnatin Libya mai samun goyon bayan MDD, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, kana dubu-dubutar fararen hula suka yi gudun hijira. Ban da wannan kuma, a ranar 12 ga watan Disamba na wannan shekara, shugaban rundunar sojojin kasar Libya mai sansani a gabashin kasar Khalifa Beiqasim Haftar ya ce, matakin da rundunar ta dauka na kai hari, da kwace Tripoli ya kusan kammala. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China