Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar kolin Libya ta amince da kudurin majalisar dokokin Turkiyya na tura dakaru zuwa kasar
2020-01-03 09:19:46        cri

Majalisar gudanarwar kasar Libya dake da sansaninta a Tripoli, ta amince da kudirin dokar majalisar dokokin kasar Turkiyya na tura dakaru zuwa kasar Libya, sakamakon yadda rikici tsakanin sojojin Libya masu sansani a gabashin kasar da dakarun sojojin gwamnati wanda MDD ke goyawa baya ke ci gaba da ta'azzara.

Tun da farko, majalisar dokokin kasar Turkiyya ta amince da kudirin doka wanda zai baiwa gwamnatin kasar damar tura dakarun sojoji zuwa kasar Libya don gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya na tsawon shekara guda, 'yan majalisar dokokin kasar 325 sun amince da kudirin yayin da mambobin majalisar 184 suka yi watsi da shi.

A ranar 27 ga watan Nuwamban 2019, kasar Turkiyya da gwamnatin Libyan mai samun goyon bayan MDD suka kulla yarjejeniyoyin fahimtar juna guda biyu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China