Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kwashe 'yan gudun hijira 124 zuwa Nijer daga Libya
2020-01-02 13:42:49        cri

Yau Alhamis hukumar kula da 'yan gudun hijra ta MDD UNHCR ta ce, ta kwashe 'yan gudun hijira 124 daga Libya zuwa Jamhuriyar Nijer.

Hukumar ta yi fatan cewa, wadannan 'yan gudun hijira za su ji dadin zama a Nijer a shekarar 2020 da muke ciki, kana hukumar za ta yi kokarin taimakawa 'yan gudun hijira wadanda ke matukar bukatar taimako, ta yadda za su bar kasar ta Libya a 'yan watanni masu zuwa.

Sakamakon tashin hankalin da ya barke a Libya da ke arewacin Afirka a shekarar 2011, ya sa dubban bakin haure yawancinsu 'yan Afirka suke kokarin ratsawa ta tekun Mediterranean daga Libya don zuwa kasashen Turai.

Hukumar ta UNHCR ta ce, yanzu haka ana tsare da bakin haure kusan 4200 a cibiyoyin tsare bakin haure a Libya. Ta kuma sha yin kira da a rufe cibiyoyin dake Libya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China