Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kai harin boma-bomai fiye da 20 ga filin jiragen saman kasar Libya
2020-01-04 17:16:41        cri
Bangaren soja na gwamnatin hadin gwiwar al'ummar kasar Libya ya sanar a jiya cewa, sojojin al'ummar kasar da Janar Khalifa Haftar yake jagoranta sun kai hare-haren boma-bomai fiye da 20 ga filin jiragen saman Mitiga da kuma yankunan dake dab da filin, lamarin ya haddasa rufewar filin jiragen saman har na tsawon wasu sa'o'i.

Janar Khalifa Haftar ya fitar da sanarwa a jiya, inda ya ki amincewa da kasar Turkiya ta tura sojoji zuwa Libya. Majalisar dokokin kasar Turkiya ta gudanar da taron gaggawa a ranar 2 ga wannan wata, inda ta amince gwamnatin kasar ta jibge sojoji a kasar Libya.

Mataimakin wakilin musamman na babban sakataren MDD dake kasar Libya Yacoub El Hillo ya yi Allah wadai da wannan lamari, wanda ya tada rikici a tsakanin sojojin al'ummar kasar da gwamnatin kasar da MDD take goyon baya, kana ya nuna damuwa ga yankunan fararen hula da kayayyakin more rayuwa da aka kaiwa hare-hare, tare da haddasa mutuwar fararen hula. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China