Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojojin kasar Libya mai sansani a gabashin kasar ta sanar da tsagaita bude wuta
2020-01-12 17:24:34        cri
Rundunar sojojin kasar Libya mai sansani a gabashin kasar a jiya Asabar ta sanar da tsagaita bude wuta tare da daina daukar duk wani matakin soja a kan gwamnatin kasar dake samun goyon bayan MDD dake yammacin kasar.

A sanarwar da ta fitar, rundunar ta ce, muddin dai gwamnati ta amince da tsagaita bude wuta, lalle su ma zasu tsagaita bude wutar, sai dai idan an karya yarjejeniyar, zasu mayar da martani mai tsanani.

Rundunar mai sansani a gabashin kasar Libya ta fara daukar matakan soja a ciki da kewayen birnin Tripoli ne a farkon watan Afrilu, a kokarin karbe iko da birnin da kuma hambarar da gwamnatin kasar dake samun goyon bayan MDD.

Dubban mutane sun mutu da kuma jin raunuka sakamakon fadan da aka gwabza, a yayin da mutane sama da dubu 120 rikicin ya raba da muhallansu.

A wata sabuwa kuma, a yau Lahadi, wasu sa'o'i bayan da rundunar ta sanar da daina daukar matakan soja, gwamnatin Libya ta amince da tsagaita bude wuta tun daga daren wannan rana. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China