Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan Afrika na goyon bayan tsarin noma ba tare da sinadarai ba domin bunkasa wadatuwar abinci
2019-06-19 10:29:52        cri

Masanan Afrika sun bayyana cewa, rungumar tsarin noma ba tare da amfani da sinadaran zamani ba ga kananan manoman Afrika, na da muhimmanci wajen magance matsalar karancin abinci da ta yanayi na karuwar yawan al'umma.

Masanan sun bayyana haka ne a wajen wani taro da aka kaddamar jiya a Nairobin Kenya, inda suka ce idan aka yi amfani da tsarin a fannin noma don kasuwanci, a fadin kasashen kudu da hamadar Sahara, zai iya samar da mafita ga tabarbarewar yanayin kasa da asarar muhallin halittu da rashin ruwa da ke tarnaki ga aikin samar da abinci.

Kasar Kenya ce ta bude taron kasa da kasa karon farko, kan amfani da dabarun kare muhallin hallitu a harkokin noma, wanda ya samu halartar masu tsara manufofi da masana da manoma da masu rajin kare muhalli.

A cewar David Amudavi, daraktan zartarwa na cibiyar Biodivision Trust mai rajin tallafawa kananan manoma, wadda ke da mazauni a Nairobi, taron da zai gudana har zuwa ranar 20 ga wata, zai samar da dandalin lalubo sabbin dabarun da ake bukata na farfado da tsarin noma ba tare da sinadarai ba, a nahiyar mafi girma na biyu a duniya.

Ya ce hada dabarun da suka dace da horar da kananan manoma, shi ne jigon inganta rungumar tsarin samar da abinci, wanda zai dace da kare muhalli a nahiyar dake fama da farin da yaki ci yaki cinyewa da kwari da cuttukan tsirrai. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China