Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan guraben aikin yi da Sin ta samar a shekarar 2019 ya kai miliyan 13.52
2020-01-14 13:53:16        cri

Ma'aikatar kula da harkokin albarkatun kwadago da na bada tabbaci ga zamantakewar al'umma na kasar Sin ya bada rahoto a yau Talata a nan birnin Beijing cewa, an samar da guraben aikin yi yadda ya kamata a shekarar 2019, yawan guraben aikin yi da aka samar bara a kauyuka da birane ya kai miliyan 13.52, yawan mutane da suka yi rajistar rasa aikin yi ya kai kashi 3.62 cikin dari. A farkon shekarar bara, gwamnatin ta tsara manufar samar da guraben aikin yi sama da miliyan 11, kuma yawan mutane da suka yi rajistar rasa aikin yi bai haura kashi 4.5 cikin dari ba, kasar Sin ta cimma manufarta yadda ya kamata. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China