Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta zama kasa ta farko a Asiya dake da rukunonin aikin ceto mai sarkakiya guda biyu da suka samu amincewar MDD
2019-10-24 14:07:56        cri

Jiya Laraba, rukunin aikin ceto na kasar Sin da kuma rukunin aikin ceton kasa da kasa na kasar Sin sun sami amincewa daga wajen MDD bayan binciken da majalisar ta yi musu, hakan ya sa, Sin ta zama kasa ta farko a Asiya dake da rukunoni dake iya gudanar da aikin ceto mai sarkakiya da ya samu amincewar MDD.

A yayin bikin mika tuta da alluna ga wadannan rukunoni biyu, mataimakin ministan hukumar kula da harkokin ko ta kwana na kasar Sin Zheng Guoguang ya nuna cewa, a matsayinta na kasar dake da irin wadannan rukunoni biyu a Asiya, Sin za ta zurfafa hadin kai da MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa don ba da gudunmawa wajen rage kalubalen da barzana da bala'u ke iya haifarwa da raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya, da kiyaye zaman rayuwar jama'a.

Wakilin ofishin daidaita kan batun jin kai na MDD Ramesh Ragasingham Mohan ya gode da taimakon da Sin take baiwa MDD a fannin aikin jin kai, kuma yana sa ran ganin karin gudunmawar da wadannan rukunoni biyu za su bayar a aikin jin kai a duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China