Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Afrika sun samu bunkasuwar cinikayyar kayan amfanin gona
2019-12-10 11:15:01        cri
Hada hadar kasuwanci kayan amfanin gona tsakanin Sin da Afrika ya ninka kusan sau goma daga shekarar 2000 zuwa 2018, kamar yadda ma'aikatar aikin gona da raya karkara ta kasar Sin ta bayyana.

Cinikayyar ta karu daga dala miliyan 650 a shekarar 2000, zuwa dala biliyan 6.92 a shekarar 2018, hakan ya nuna cewa ana samun karuwar kashi 14 bisa 100 a duk shekara, ministan aikin gona na kasar Sin Han Changfu, shi ne ya bayyana hakan a taron dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika game da raya aikin gona karo na farko wanda aka bude a ranar Litinin a birnin Sanya dake kudancin kasar Sin.

Han ya ce, sassan hukumomin bunkasa aikin gona na Sin da kasashen Afrika sun kulla hadin gwiwa bisa tushen mutunta juna, da samar da daidaito, hakan ya samar da moriya ga bangarorin ciniki, da zuba jari, da mu'amala tsakanin mutum da mutum, da bada horo game da fasahohin zamani.

Dandalin wanda aka kaddamar, ya samu mahalarta kusan 500, da suka hada da wakilan cibiyoyin bincike da manyan makarantun ilmi, da kamfanonin cikin gida da na kasashen waje, har ma da hukumomin kasa da kasa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China