Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sashen samar da aikin yi na kasar Sin ya samu daidaito cikin watanni 10
2019-11-14 14:00:11        cri
Hukumar kididdiga ta kasar Sin ko NBS a takaice, ta ce sashen samar da aikin yi na kasar Sin, ya samu daidaito cikin watanni 10. NBS ta fidda wannan alkaluma ne a Alhamis din nan. Alkaluman sun nuna cewa, cikin watannin 10 na baya bayan nan, an kirkiro guraben ayyukan yi a birane har miliyan 11.93, wanda hakan ya yi daidai da bukatar da ake da ita, ta samar da karin ayyukan yi miliyan 11.

A wani ci gaban kuma, binciken ya nuna cewa, a watan Oktoba, alkaluman rashin ayyukan yi a manyan biranen kasar 31 ba su wuce kaso 5.1 bisa dari a watan Oktoba ba, adadin da ya ragu da kaso 0.1 bisa dari kan adadin da aka samu a watan Satumba.

Ana samar da alkaluman sakamakon binciken marasa ayyukan yi a birane ne, ta hanyar lissafa mutanen da ba su da ayyukan yi, wadanda kuma suka shiga bincike da ake gudanarwa a sassan birane, ciki hadda 'yan ci rani dake shigowa birane daga yankunan karkara.

A shekarar 2014 ne dai aka fara gudanar da wannan bincike, da nufin samar da ainihin abun da sashen samar da ayyukan yi ke ciki, da kuma amfani da shi wajen kara tattara bayanan marasa ayyukan yi a birane, kari kan wanda ma'aikatar lura da al'amuran al'umma da tsaron cikin gida ke samarwa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China