Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta dauki matakan tabbatar da samar da ayyukan yi
2019-12-05 11:03:42        cri

Kasar Sin za ta dauki matakai da dama a lokaci guda, domin tabbatar da samar da guraben ayyukan yi na tafiya ba tare da tangarda ba. Gwamnati za kuma ta zage damtse wajen mara baya ga ayyukan wucin gadi da bunkasa damammakin aikin yi ga mutane masu bukata ta musammam da kuma magance matsalar biyan hakkokin da ma'aikata masu kaura ke bi bashi, bisa hanyoyi na shari'a.

An yanke shawarar daukar matakan daban-daban ne yayin taron majalisar zartarwar kasar da ya gudana jiya Laraba, karkashin jagorancin Firaminista Li Keqiang.

Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a watan da ya gabata, sun nuna cewa, a watanni 10 na farkon bana, an samar da sabbin guraben ayyukan yi miliyan 11.93 a birane, wanda ya cimma mizanin da aka sanya na miliyan 11 kafin cikar wa'adin da aka diba. Nazarin yawan rashin aikin yi a birane a matakin kasa na watan Oktoba, ya tsaya kan kaso 5.1, wanda ya sauka da kaso 0.1 a kan na watan Satumba.

An kuma jaddada yayin taron na jiya cewa, dole ne gwamnatocin yankuna su mara baya ga samar da ayyukan yi. Ana bukatar su bullo da karin matakan da za su samar da guraben ayyukan yi da magance dukkan abubuwan dake tarnaki ga ayyukan wucin gadi.

Har ila yau, za a kara zage damtse wajen bunkasa fara sana'o'i da kirkire-kirkire. Za kuma a saukaka ka'idojin ba da rance ga masu kanana da matsakaitan sana'o'i. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China