Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta gudanar da taron tsara shirin bunkasa yankunan karkara na shekarar 2020
2019-12-21 20:21:47        cri
An gudanar da babban taron tsara manufofin raya yankunan karkara a Beijing tsakanin ranakun 20 zuwa 21 ga watan Disamba, inda aka tsara jadawalin shirin raya kasa a fannonin aikin gona, da raya yankunan karkara, da kyautata rayuwar mazauna yankunan karkara na shekara mai zuwa.

An nazari kan jawabin shugaba Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiyar jamiyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC) a lokacin taron.

Shugaba Xi ya gabatar da jawabin ne a yayin taron kwamatin hukumar siyasa na kwamitin tsakiyar JKS, inda daga bisani aka nazarci muhimman batutuwan da jawabin ya kunsa musamman batutuwan da suka shafi aikin gona, raya yankunan karkara da kuma kyautata rayuwar mazauna karkara. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China