Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta gabatar da kan sarki na murnar sabuwar shekara ta bera bisa kanlandar gargajiya ta kasar Sin
2020-01-14 10:01:40        cri

Ofishin kula da harkokin gidan waya na MDD ya gabatar da kan sarki na musamman na murnar sabuwar shekara ta bera bisa kanlandar gargajiya ta kasar Sin.

Takardar kan sarki na kunshe da kan sarki 10, kowanensu ya kai darajar dala 1.2, kuma baki dayan takardar ta kai dala 14.95.

Rabin bangaren hagu na kan sarki, launin shudi ne dake almantar MDD, yayin da rabin daman sa alamar bera ne bisa fasahar yanke takarda. Masanin zane na kasar Sin Yin Huili shi ne ya zana alamar bera, kuma ya yi amfani da launukan zinari da ja, wadanda suke da babbar ma'ana da alaka da bikin bazara na kalandar gargajiya ta kasar Sin.

Rahotanni na cewa, a watan Mayun shekarar 2010, ofishin ya soma gabatar da kan sarkin dabobbi na sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya karo na farko, don murnar cika shekaru 30 da Sin ta gabatar da kan sarkin dabobbi na sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya. Kan sarki na bera da MDD ta gabatar, shi ne kan sarki na dabobbi karo na 11 da majalisar ta fitar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China