Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na neman tawagar bincike ta MDD ta girmama 'yancin kan Iraki
2019-11-27 09:54:11        cri

Wakilin kasar Sin, ya yi kira ga tawagar dake binciken laifukan kungiyar IS ta MDD wato UNITAD dake Iraki, ta girmama cikakken 'yancin kasar.

Mataimaikin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya ce ya kamata UNITAD ta girmama cikakken 'yancin Iraki tare da ikonta a kan laifukan da aka aikata a yankinta.

UNITAD tawaga ce ta bincike ta MDD dake da nufin tabbatar kungiyar IS ta dauki alhakin dukkan laifukan da ta aikata.

Wu Haitao ya bayyanawa kwamitin sulhu na MDD cewa, ya kamata tawagar ta taka muhimmiyar rawa wajen karfafa karfin gwamnatin Iraki, ta yadda za ta iya kama kungiyoyin ta'addanci da laifukan da suka aikata.

Yiwuwar tawagar UNITAD ta iya magance sabbin kalubale ya dogara ne kan karfinta na rike matsayinta na mai tsare gaskiya da adalci, kuma mai zaman kanta, tare kuma da neman goyon bayan al'ummar kasar.

Shugaban tawagar Karim Khan ne ya yi wa kwamitin sulhu na MDD bayani game da ayyukan tawagar da aka dorawa nauyin taimakawa kokarin Iraki, na ganin IS ta dauki alhakin laifukan da ta aikata, ta hanyar tattarawa da adana bayanai da shaidun laifukan kungiyar na yaki da na keta hakkin dan Adam da kisan kiyashi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China