Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ba ta son kalubalantar wani, adawa da wani, ko maye gurbin wani, in ji jakadan Sin a Burtaniya
2019-12-09 10:54:49        cri
Jiya Lahadi, jakadan kasar Sin dake kasar Burtaniya Liu Xiaoming, ya gabatar da wani sharhi a jaridar The Sunday Telegraph ta kasar Burtaniya, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana dukufa wajen gina tsarin tattalin arziki mai bude kofa ga waje, kuma ba ta son kalubalantar wani, ko adawa da wani, ko kuma maye gurbin wani.

Cikin sharhin, an ce, kwanan baya, wasu jami'ai da masana na kasashen yammacin duniya, sun yi kira ga mambobin kungiyar tsaro ta NATO da su yi hadin gwiwa don nuna adawa da kasar Sin, bisa zargin cewa wai kasar Sin ta zama babban kalubale gare su. Dangane da hakan, Li Xiaoming ya ce, wannan damuwa ba ta da tushe, kuma an bayyana wannan damuwa ne domin rashin fahimtar kasar Sin.

Liu Xiaoming ya jaddada cewa, da farko, kasar Sin za ta ci gaba da neman bunkasuwarta cikin zaman lafiya, kuma ba ta son kalubalantar wani. Wannan shi ne babban alkawarin da kasar Sin ta yi wa kasa da kasa. Sa'an nan kuma, kasar Sin tana son neman dauwamammen ci gaba cikin hadin gwiwarta da kasa da kasa, tare kuma bisa dukkan fannoni, kana ba za ta nuna adawa ga wani ko wata ba. A karshe dai, kasar Sin tana neman bunkasuwar kasa ba tare da boye komai ba, kana, ba ta son maye gurbi na wani ko wata.

Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da kasancewa kasa mai tasowa mafi girma a duniya, tana kuma dukufa wajen biyan bukatu na al'ummomi biliyan 1.4, da kyautata zaman rayuwarsu, wannan shi ne babban nauyin dake gaban gwamnatin kasar Sin. Kuma gudanar da ayyukanta yadda ya kamata, zai zama babbar gudummawar da za ta samar wa dukkanin bil Adama, kana shi ne babban nauyin da Sin ta dauka wa kasa da kasa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China