Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yang Jiechi ya zanta da sakataren harkokin wajen Amurka ta wayar tarho
2019-12-07 20:30:38        cri
Yau Asabar mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma daraktan ofishin kwamitin kula da harkokin ketare na kwamitin tsakiya Yang Jiechi ya zanta da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo.

A yayin zantawar, Yang ya jaddada cewa, a cikin 'yan kwanakin da suka wuce, kasar Amurka ta sanya hannu kan wata doka kan hakkin dan Adam da demokuradiyya na Hong Kong, da kuma zartas da dokar hakkin bil Adama game da jihar Xinjiang ta Uygur ta shekarar 2019, matakan da kasar ta dauka sun keta dokokin kasa da kasa.

Kasar Sin ta bukaci bangaren Amurka da ya fahimci hakikanin halin da ake ciki, da gyara kuskurensa, da kuma dakatar da jirkita gaskiya da bata sunan kasar Sin, da dakatar da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China