Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan Birtaniya: Sin za ta samun bunkasuwa mai sauri a cikin shekaru 10 masu zuwa
2020-01-07 15:20:08        cri

 

Shafin yanar gizo na jaridar Guardian ta kasar Birtaniya, ya wallafa wani bayani da babban manazarcin jami'ar Cambridge Martin Jacques ya gabatar. Bayanin ya nuna cewa, Sin ta samu bunkasuwa mai sauri a shekaru 10 da suka gabata, kuma za a ci gaba da samun bunkasuwa mai sauri a cikin shekaru 10 masu zuwa. Bayanin dai ya samu karbuwa sosai a kan Intanet.

Martin Jacques ya wallafa wannan bayani ne a kan shafin Twitter, mutane da dama na tura shi zuwa sabbin shafuka, da kuma amince da shi. Wani ma ya nuna cewa, babu kuskure ko yaudara a cikin bayanin, domin labari ne na gaskiya, wanda ba a samun irin sa a kullum ta kafofin yada labarai na kasashen yamma.

Ban da wannan kuma, wani ya nuna cewa, kasa mai yawan mutane biliyan 1.4 dake da makoma mai haske ta fuskar tattalin arziki, abin lura shi ne, ba ta cin zarafin saura kasashe, matakin da ya shaida karfinta na ba da jagoranci.

Dadin dadawa, wani ya nuna cewa, yana fatan abin haka yake, sabo da ana bukatar kawar da yake-yake da kara hadin kai, wanda hakan zai amfani dukkanin Bil Adam.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China